Isa ga babban shafi
rahotanni

An shiga damuwa a Nijar bayan da SONITRAV ya dakatar jigila zuwa Burkina

A Jamhuriyar Nijar kamfanin sufurin jama’a na SONITRAV ya dakatar da bin hanyar da ta tashi daga Yamai zuwa Wagadugu kasar Burkina Faso, matakin da ya fara aiki tun daga ranar 15 ga wannan watan na yuni. Shugabannin kamfanin sun ce sun dauki matakin ne domin kare lafiya da rayuwar fasinjojinsu. Tuni dai wannan mataki ya soma yin tasiri ga zirga zirga tsakanin kasashen biyu. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton wakilinmu Baro Arzika.

Taswirar dake nuna sassan Jamhuriyar Nijar da wasu kasashe makwafta.
Taswirar dake nuna sassan Jamhuriyar Nijar da wasu kasashe makwafta. © USAID/FFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.