Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta kori jaridar Juene Afrique ta Faransa daga kasar

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da sallamar mujallar Jeune Afrique daga kasar kwata-kwata, bisa zargin ta da wallafa labaran karya, labaran da ta ce sun tayar da hankulan jama’a.

Taswirar kasar Burkina Faso
Taswirar kasar Burkina Faso © RFI
Talla

Sallamar mujallar Jeune Afrique na zama wani mataki na baya-bayan nan da Burkina Faso ta dauka kan kafafen yada labaran da ke da alaka da Faransa, tun bayan juyin mulkin sojoji a bara.

Ta cikin sanarwar da gwamnatin sojin ta fitar, ta ce ta lura mujallar na mayar da hankali wajen wallafa labaran da ke bata mutuncin sojojin da kuma yi musu kage, da nuna cewa sun gaza wajen tafiyar da kasar musamman ta fannin tsaro.

Labaran wasu munanan hare-hare da jaridar ta ce ‘yan ta’adda sun kai sassan kasar cikin kwanaki hudun da suka gabata sun haifar da fargaba da cece-kuce bayan da suka fito da gazawar sojojin karara, dalilin da ya sa suka dauki matakin sallamar ta.

Tun a baya sojojin suka sallami kafafen yada labarai na Faransa, da suka hadar da Radio France International da kuma France 24, bisa zarginsu da yada labaran da suke goyawa ‘yan ta’adda baya a fakaice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.