Isa ga babban shafi

Najeriya na duba yiwuwar dage haramcin barasar leda da roba

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta duba yiwuwar dage dokar hana barasar da ake yi na leda da wadda ake yi a kananan roba da ta ayyana watan Janairun wannan shekara. 

Hoto don misali.
Hoto don misali. AP - Emilio Morenatti
Talla

Jaridar The Nation da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa, hakan ya biyo bayan zanga-zangar lumana da kungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin barasa da tabar sigari suka gudanar a harabar ma'aikatar lafiya ta kasar, a jiya Laraba.

Yayin zanga-zangar, ma'aikatan sun bayyana irin halin kunci da matakin gwamnatin ya jefasu ciki na datse musu hanyar cin abincinsu. 

A karshen watan Janairun da ya gabata ne hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya "NAFDAC"  ta sanar da haramta yi da sayar da irin wadannan barasa, duba da illar da za su yi wa tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasar nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.