Isa ga babban shafi
Kano-Hisbah

Matasan Kano sun yi arangama da 'yan Hisba saboda barasa

Matasan Kano sun yi arangama da jami’an Hisbah a yankin Sabon Gari sakamakon samamen da jami’an suka kai kan wani shagon sayar da barasa.

Jami'an Hisba na fasa kwalaben giya a Kano
Jami'an Hisba na fasa kwalaben giya a Kano © 247ureports
Talla

Rahotanni na cewa, jami’an na Hisbah sun dirar wa shagon Ballat Hughes a yammacin jiya Talata tare da kwace kayayyakin maye da wata mata ke sayarwa, abin da ya fusata matasan har suka yi fito-na-fito da ‘yan Hisban.

Hukumomin jihar Kanon ta Najeriya sun haramta sha da kuma sayar da kayayyakin maye  a karkashin dokar Shari’ar Musulunci , amma a mafi tarin lokuta, wannan doka ba ta cika yin tasiri ba kan mazauna Sabon Gari, yankin da akasari baki ‘yan kudancin kasar ke rayuwa.

Rahotanni na cewa, matasan sun yi ta kone-kone tare da datse hanyoyi a yayin tashin hankalin da jami’an na Hiusbah.

Kazalika rahotannin sun ce, ‘yan jagaliya sun yi amfani da wannan dama wajen kaddamar da farmaki kan wasu shaguna tare da sace kayayyakin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.