Isa ga babban shafi

Libya: Har yanzu ana ganin mayakan 'yan tawaye a birnin Tripoli

Rahotanni na cewa ana ci gaba da ganin mayakan kungiyoyi masu dauke da makamai a titunan babban birnin Libya, Tripoli bayan da gwamnatin hadin kan kasa a kasar ta ce ta amince da janye shingayen bincike da sintiri a cikin makonni masu zuwa.

hukumomin kasar sun ce za su ci gaba da sa idanu kan duk wata zirga-zirgar 'yan tawayen saboda sha'anin tsaro.
hukumomin kasar sun ce za su ci gaba da sa idanu kan duk wata zirga-zirgar 'yan tawayen saboda sha'anin tsaro. © AFP
Talla

Tun a shekarar 2011 kungiyoyi masu dauke da makamai suka yi ta rikicin karbe iko da kasar, biyo bayan kisan tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, lamarin da ya sa ka shafe shekaru da dama cikin yanayi na tashin hankali da rashin tsaro.

A ranar Laraba ministan harkokin cikin gida na kasar, Emad Trabulsi, ya sanar da cewa, kungiyoyin masu dauke da makamai da ke birnin Tripoli sun amince su janye dakarunsu kafin karshen watan azumin Ramadan.

Trabulsi ya kuma ce, duk da cewa tsarin yana cike da sarkakiya, amma dukkanin kwamandoji da jami'an tsaro a shirye suke don samun nasarar aikin hukumomin tsaro.

Ya ce, ko da a ce bangarorin da ke dauke da makamai ba su bayyana kansu a kan tituna ba, ana ganin ba za a yi watsi da duk wani yunkuri na ficewar su daga kasar ba tare da cimma matsaya kan makomar siyasar Libya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.