Isa ga babban shafi

Mahukuntan Libya sun gano makeken kabari a Sirte

Mahukuntan Libya sun gano gawarwaki 18 da aka binne a wani kabari da ke garin Sirte a gabar tekun kasar, birnin da ya kasance tsohon sansanin kungiyar ISIS.

Daya daga cikin manyan kaburburan da aka rika ganowa a yankunan da suka taba kasancewa a karkashin ikon mayakan ISIS a Libya.
Daya daga cikin manyan kaburburan da aka rika ganowa a yankunan da suka taba kasancewa a karkashin ikon mayakan ISIS a Libya. © REUTERS/Ayman Al-Sahili
Talla

An tono gawarwakin ne a yankin Sabaa da ke garin na Sirte, daga bisani kuma aka kai su wani asibiti a yankin.

A sanarwar da ta fitar ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ba da agajin gaggawa ta Libya ta kara da cewa, jami’an ta sun tattara samfurin kasusuwan da aka gano domin gano gawarwakin wadanne mutane ne aka binne, ba tare da bayar da karin bayani kan musabbabin mutuwar su ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake gano gawarwaki da dama cikin kabari guda a Sirte ba, domin ko a watan Oktoba, sai da jami’ai suka ganho gawarwakin mutane 42 cikin wani makeken kabari a wata makaranta da ke birnin.

Yaushe ISIS ta kwace iko da Sirte?

A shekarar 2015 kungiyar ISIL ta kwace iko da birnin Sirte, inda ta yi amfani da damar da ta samu a rikicin da ke tsakanin bangarori daban-daban na tsaffin ‘yan tawaye da suke neman zama masu karfin fada a ji a yankin, bayan taimakon da suka samu daga kungiyar tsaro ta NATO, wajen kashe tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.

A shekarar 2016, dakarun da Amurka ke marawa baya wadanda ke kawance da gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya mai hedikwata a Tripoli, suka fatattaki ISIL daga birnin Sirte, mahaifar Gaddafi.

A halin yanzu kuma daruruwan mutanen da ake zargin tsoffin mayakan ISIL ne, na ci gaba da zama tsare a gidajen yari, inda da yawa ke jiran shari’a.

Birnin Sirte a yanzu yana hannun babban Kwamanda Khalifa Haftar ne da ya ja tunga a gabashin kasar, wanda kuma ke neman kifar da gwamnatin Tripoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.