Isa ga babban shafi

Libya: Rikicin birnin Tripoli ya kara kamari a bana

Wani sabon rikici da ya barke a birnin Tripoli na Libya ya tilastawa mutane zama a gidajen su tsawon kwanaki, lamarin da ke haddasa musu yunwa da kuma mutuwar wasu da ke bukatar agajin likita cikin gaggawa. 

Motar dakarun Libya na 444 Brigade da ke goyon bayan gwamnatin hadin kai da aka dauka a birnin Tripoli ranar 27 ga watan Agusta, 2022.
Motar dakarun Libya na 444 Brigade da ke goyon bayan gwamnatin hadin kai da aka dauka a birnin Tripoli ranar 27 ga watan Agusta, 2022. © AYMAN AL-SAHILI/REUTERS
Talla

Ma’aikatar Lafiyar kasar ta cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce wannan shine rikici mafi muni da ya tashi a kasar cikin wannan shekara, kuma ya zama dole gwamnati ta dauki mataki, idan kuma ba haka ba zai dauki sabon salo. 

Bayanai sun ce rikicin ya tashi ne a tsakanin wasu kungiyoyin masu rike da makamai, tun bayan da bangare daya suka zargi daya bangaren da tsare kwamandan su a filin jirgin saman Tripoli. 

Hukumar lafiya ta birnin Tripoli ta ce mutane 27 ne suka mutu yayin da fiye da 100 suka jikkata a tashin hankalin, ba tare da cewa adadin ya hada da mayaka da fararen hula ba.

Dakarun kare kai na musamman da na Brigade 444 na daga cikin dakarun soji mafi karfi a birnin Tripoli, kuma fadan da suka yi da ya yi mafari tun da yammacin ranar litinin din da ta gabata, ya girgiza gundumomi a fadin babban birnin kasar.

Bangarorin biyu dai sun goyi bayan gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa a rikicin bara, kuma fadan da suka yi na ba zato ba tsammani kawo karshen kwanciyar hankali da aka samu tsawon watanni a birnin Tripoli, lamarin da ya kara dagula lamuran da ke tattare da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.