Isa ga babban shafi

Kotun Libya ta yanke hukuncin kisa ga wasu tsoffin ‘yan kungiyar IS

Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 17 bayan samunsu da laifin shiga kungiyar IS da kuma aikata ta’asa da sunanta, kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana.

Amurka ta ba da gudummawar sojoji kusan 2,000 ga wani shirin kawance don kawo karshen ISIL
Amurka ta ba da gudummawar sojoji kusan 2,000 ga wani shirin kawance don kawo karshen ISIL AFP PHOTO / HO / ISIL
Talla

Kotun ta Tripoli ta kuma yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga mutane biyu, yayin da wasu 14 kuma ta yanke musu hukuncin zaman gidan na karamin lokaci.

Sanarwar ta ce, an same su da laifin wasu ayyukan da ke da alaka da kungiyar IS da kuma kai hari kan gwamnati da zaman lafiyar jama'a da kuma haifar da tashe-tashen hankula a yammacin birnin Sabratha da kewaye.

Wadanda aka gurfanar din an same su da laifin kashe jimillar mutane 53, tare da lalata gine-ginen gwamnati da kuma batar da mutane da dama. Ko da yake ba a bayyana sunayen wadanda aka yankewa hukuncin kisa ba.

Libya ta fada cikin tashin hankali bayan boren da ya kifar da gwamnatin Moamer Kadhafi a shekara ta 2011 abin da ya haifar da tabarbarewar madafun iko inda dimbin kungiyoyi masu dauke da makamai ciki har da IS suka mamaye kasar.

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta yi amfani da garin Sirte na Kadhafi a matsayin sansaninta tun daga tsakiyar shekara ta 2015 har zuwa lokacin da aka kawar da ita a shekarar 2016.

An kashe wasu masu jihadi, tare da kama wasu, wasu kuma sun nemi mafaka ne a garuruwan  da ke yammacin Libya.

Mayakan IS sun kuma kwace Sabratha na wani dan lokaci a cikin watan Fabrairun 2016, amma cikin kankanin lokaci sojojin gwamnati suka fatattake su.

A shekara ta 2010 ne Libiya ta kada kuri'ar kin amincewa da wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a dakatar da hukuncin kisa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.