Isa ga babban shafi
RIKICIN SUDAN

Sudan ce kan gaba a sahun kasashen mafi yawan 'yan gudun hijira - OCHA

Hukumar  dake kula da ayyukan jinkai  ta  Majalisar dinkin duniya Ocha ta bayyana cewa,  Sudan ce  sahun gaba wajen  yawan  ‘yan gudun hijira a duniya inda a yanzu haka ta ke da ‘yan gudun hijira miliyan 6 jibge a sansanoni daban-daban dake cikin  kasar.

Біженки з Судану плачуть, дізнавшись про загибель родичів
Біженки з Судану плачуть, дізнавшись про загибель родичів © El Tayeb Siddig / Reuters
Talla

Adadin ‘yan gudun hijirar ya kara cirawa ne a   a cikin watan decembar bara,  a yayin da ake fafutukar isar da kayayyakin agajin jinkai ga  jama’ar dake cikin matukar bukata,  duk da karancin kudade da kungiyoyin ba da agajin ke fuskanta.

Saboda yawan ‘yan gudun hijirar ake samun dandazon jama’a domin karbar kudade da wata kungiya mai zaman kanta ke yi ga mutanen da suka tsere wa yakin na Sudan a sassa kasar mai tazarar kimanin  kilomita goma sha biyar arewacin  Rubkona tun a ranar 30 ga Oktobar shekara ta 2023.

A yanzu haka dai  Sudan ce,  ke rike da kambun Kasa mai mafi yawan adadin wadanda suka tsere daga yankunansu a sanadiyar yake yake.

Yawan adadin mutanen yasa aka rarraba su zuwa sansanoni sama da dubu 6 da dari 2 a jihohi goma sha 8 na kasar domin a sama masu natsuwa yadda ta kamata.

Sai dai kayakin agajin ba za su iya karade dukkanin inda ‘yan gudun hijirar ke zaune ba, saboda rashin cikkaken tsaro da satar dukiyar jama'a, da katse hanyoyin sadarwa, da rashin isashen kudi da kuma karancin kayan aiki da ma'aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.