Isa ga babban shafi

Sudan ta yiwa jakadanta da ke Kenya kiranye

Gwamnatin Sudan ta umarci jakadanta na kasar Kenya da ya koma gida bayan da kasar ta karbi bakunci jagoran dakarun RSF Muhammad Dagalo. 

Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban gwamnatin sojin Sudan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban gwamnatin sojin Sudan. © AFP PHOTO / HO/ SAUDI PRESS AGENCY
Talla

 

Dagalo wanda shi ne ke jagorantar dakarun RSF a yakin da suke gwabzawa da gwamnatin kasar ya fara wata ziyarar karfafa alaka da kasashe makwafta ciki kuwa har da kasar Kenya. 

Kasashen da ya ziyarta zuwa yanzu sun hadar da Uganda, Ethiophia, da Djibouti da Kenya kuma yanzu haka yana Africa ta kudu, dalilin da ya fusata shugaba Al-Burhan wanda sojojin sa suka rasa iko da wasu yankuna a hannun dakarun RSF. 

Ta cikin wata sanarwa da Kamfanin DillancinLabaran kasar ya wallafa, ta ce ministan harkokin waje Ali-Al-Sadiq ya umarci jakadan Sudan a Kenya ya koma gida, abinda ke nufin alaka ta sami rauni tsakanin kasashen biyu. 

Sanarwar ta ce nan gaba kadan gwamnatin za ta tsayar da matsayar ta game da yanke duk wata hulda da Kenya ko kuma kasin hakan. 

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da jagoran na RSF  ya ce a shirye yake ya tsagaita wuta kan rikicin da aka shafe watanni ana tafkawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.