Isa ga babban shafi

Jagoran RSF na ziyara a Habasha da Uganda don sasanta rikicin Sudan

Jagoran dakarun kai daukin gaggawa na RSF a Sudan Mohamed Hamdan Daglo ya isa birnin Addis Ababa fadar gwamnatin Habasha yau Alhamis, a wata ziyara da ta kai shi har Uganda, irinta ta farko da ta fitar da shi daga Khartoum tun bayan faro yakin kasar a watan Aprilun shekarar nan.

Jagoran dakarun RSF a Sudan Mohammed Hamdan Daglo.
Jagoran dakarun RSF a Sudan Mohammed Hamdan Daglo. © capture d'écran/lemonde.fr/afrique
Talla

Ziyarar ta Mohamed Hamdan Daglo a Habasha da Uganda wani bangare ne na yunkurin da kasashen makwabtan ke yi don ganin sun shirya wata tattaunawa tsakaninshi da jagoran mulkin Soji Abdel Fattah al-Burhan da nufin kawo karshen yakin na Sudan.

Janarorin Sojin biyu har zuwa yanzu basu kai ga haduwa fuska da fuska ba, tun bayan barkewar yakin na Sudan a watan Aprilu da ya lakume rayukan mutane fiye da dubu 12 baya ga tilastawa miliyoyi tserewa daga matsugunansu.

Ma’aikatar harkokin wajen Habasha ta wallafa batun ziyarar ta Daglo a shafinta na X wanda ya samu tarba daga mataimakin Firaministan kasar Demeke Mekonnen ko da ya ke sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan batutuwan da ziyarar ta kunsa ba.

Ziyarar ta Daglo zuwa Habasha a yau na zuwa ne bayan makamanciyarta a Uganda jiya Laraba, inda ya gana da shugaba Yoweri Museveni.

Mohamed Hamdan Daglo ya bayyana cewa a shirye ya ke ya shiga duk wata tattaunawa da za ta kai ga kawo karshen yakin da kuma sake gina kasar.

Kowanne lokaci daga yanzu ne kuma ake saran yiwuwar jagoran dakarun na RSF ya kai ziyara Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.