Mayakan RSF sun karkata hare-harensu zuwa sassan kudancin Sudan
An shiga wani yanayi na fargaba a sassan Sudan, bayan da mayakan RSF suka fara karfi a kudancin kasar, yankin da a baya rikicin na kusan watanni 8 bai kai gareshi ba, matakin da ke zuwa kwana guda bayan dakarun sojin kasar sun sanar da dakile hare-haren mayakan tare da fatattakarsu daga Wad Madani.
Wallafawa ranar:
A karshen makon jiye ne motocin mayakan RSF suka fara kutsa kai yankin na kudanci lamarin da ya sanya fargaba a zukatan al’ummar Al-Jazira musamman kauyukan da ke arewacin Wad Madani, fadar gwamnatin jihar mai dauke da ‘yan gudun hijira fiye da miliyan guda wadanda suka tserewa yakin kasar na kusan watanni 8 daga yankunansu.
Rabab wata mazauniyar yankin ta shaidawa AFP cewa yankin na shirin komawa dandalin yaki tsakanin mayakan na RSF da Sojin Sudan, bayan da ko a Asabar din da ta gabata mayakan suka kashe fararen hula akalla 8.
Wani ganau da shima ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron mayakan RSF wadanda suka yi kaurin suna wajen kisan fararen hula, ya shaidawa AFP cewa mayakan sun harbe mutanen ne lokacin da suka nemi dakatar da su daga satar kayakin jama’a.
Daga kudancin Khartoum kadai akwai fiye da fararen hula rabin miliyan da ke gudun hijira a Wad Madani bayan da yaki ya daidaita fadar gwamnatin kasar.
Zuwa karshen watan Nuwamban da ya gabata, alkaluman mutanen da aka kashe a yakin na Sudan cikin watanni 8 ya kai mutum dubu 12 da 190 yayinda miliyoyi ke hijira a ciki da wajen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu