Isa ga babban shafi

Al-Burhan ya gindaya sharudda gabanin shiga tattaunawa da jagoran RSF

Jagoran mulkin Sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya gindaya sharudda gabanin amincewa da shiga tattaunawa da bangaren jagoran dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo da suka shafe fiye da watanni 9 suna gwabza yaki.

Janar Abdel Fattah al-Burhan daga yamma tare da janar Mohamed Hamdan Daglo.
Janar Abdel Fattah al-Burhan daga yamma tare da janar Mohamed Hamdan Daglo. © AP
Talla

Tun farko jagoran na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, da kansa ya mika bukatar tattaunawar don samar da zaman lafiya a kasar wadda yaki ya daidaita, sai dai a Lahadin da ta gabata, bangaren gwamnatin Sojin ta Sudan ta bayyana cewa tattaunawar ba za ta yiwu ba har sai RSF ta aminta da jerin shardodin da al-Burhan ya gindaya.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar, ta bayyana cewa wajibi RSF ta jagoranci aikin kwashe ilahirin mayakanta da yanzu haka ke zaune a gidajen fararen hula gabanin shiga tattaunawar.

Haka zalika al-Burhan ya bayyana cewa dole ne RSF ta koma biyayya ga yarjejeniyar birnin Jedda da bangarorin biyu suka cimma a ranar 11 ga watan Mayun 2023.

A cewar sanarwar har sai RSF ta janye ilahirin dakarunta da ke jihar al-Jazeera ne tukuna gwamnatin Sojin za ta yarda cewa da gaske ta ke a tattauanwar.

Zuwa yanzu RSF ke rike da galibin yankunan Sudan ciki har da na yankin kudu maso gabashin kasar wanda a baya yakin bai kai ga can ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.