Isa ga babban shafi

EFCC ta gayyaci tsohuwar minista a Najeriya kan zargin wawure kusan Naira biliyan 40

Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Najeriya ta gayyaci tsohuwar ministar jin kadi da takaita aukuwar ibtila’I ta kasar Hajiya Sadiya Umar Farouk kan zargin ta da karkatar da sama da naira biliyan 37, ko kuma aka karkatar da su a karkashin ikonta.

Hajiya Sadiya Umar Farouk tsohuwar ministar ayyukan jinkai a Najeriya.
Hajiya Sadiya Umar Farouk tsohuwar ministar ayyukan jinkai a Najeriya. NAN
Talla

Hukumar ta bukaci ministar ta amsa gayyatar a shalkwatar ta da ke babban birnin kasar Abuja ranar laraba mai zuwa don yin cikakken bayani game da yadda wadannan kudi suka bata ko sama ko kasa.

Sadiya Faruk na cikin ministocin Buhari da aka rika zargin su da cin hanci tun suna kan karagar mulki, duk da dai ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata.

EFCC din ta zargi Sadiya da hada kai da wani mutum mai suna James Okwete wajen wawure wadannan kudi, sai dai tuni Sadiyar ta ce ko sunan mutumin bata taba ji ba.

Bayanai na nuna cewa James ya shafe kusan kwanaki 10 a hannun jami’an na EFCC, inda suke gudanar da bincike.

Daga tsohuwar ministar har masu bata shawara da mataimakanta kan harokin yada labarai sun ki yiwa manema labarai karin haske kan wannan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.