Majalisar Dinkin Duniya na neman kudade don magance matsalar 'yan gudun hijira a duniya
Wasu alkaluma da ake da su na bayyana cewa duk da girman rikicin Gaza, bai kamata kasashen duniya su manta da dubun-dubatar ‘yan gudun hijira a duniya ba, kalaman Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira, Filippo Grandi, a wajen bude taron kolin ‘yan gudun hijira na duniya, wanda ke gudana har zuwa ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekara a Geneva.
Wallafawa ranar:
Minti 2
Talla
Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira, Filippo Grandi ya bayyana damuwa matuka," ,ya kuma bayyana cewa, ya zama wajibi hukumar ta sallami kusan mukamai 900 daga cikin 20,000.
Ya zuwa wannan lokaci kungiyar ta na bukatar dala miliyan 400 kusan (Euro miliyan 371) nan da karshen shekara.
Yaki a Ukraine, tashe-tashen hankula a Sudan, Habasha, rikicin jin kai a Afghanistan,hukumar ta fitar da wasu alkaluma inda ta ke cewa sama da mutane miliyan 114 ne suka rasa matsugunansu a fadin duniya a karshen watan Satumba.
Rahoto daga Hukumar na nuni yawan ‘yan gudun hijira a duniya ya ninka a cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya kai mutane miliyan 36.4 a tsakiyar shekarar 2023.
Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa "babban bala'in bil'adama na faruwa a zirin Gaza", kuma ya yi hasashen "karin mutuwa da wahala a tsakanin fararen hula, da kuma kara yawan yan gudun hijirar daga yankin.
Sai dai jami'in ya saba sukar kasashen da a idonsa ba sa bude kofofinsu ga 'yan gudun hijira.
Ya sake yin nuni da cewa a ranar Laraba shirin gwamnatin Burtaniya na mai da hankali kan korar bakin haure da suka isa Birtaniya ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Rwanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu