Isa ga babban shafi

Karancin ruwa ya hallaka giwaye 100 a babban gandun dajin Zimbabwe

Akalla giwaye 100 sun mutu a babban gandun dajin kasar Zimbabwe a sakamakon fari da karancin ruwa da ya addabi dabbobin kasar.

Zimbabwe ce ke kan gaba a yawan giwaye a Nahiyar Africa
Zimbabwe ce ke kan gaba a yawan giwaye a Nahiyar Africa AFP - LUIS TATO
Talla

Wata kungiyar kasa da kasa da ke kula da walwalar dabbobi ta ce halin da manyan dabbobi ke ciki a Zimbabwe saboda fari abin tausayi ne, don haka ya zama wajibi a dauki matakin da ya dace.

Kungiyar ta ce kawo yanzu an sami rahoton mutuwar giwaye 100 a babban gandun dajin Hwange.

Gandun dajin Hwange mai fadin kilomita dubu 14,600 na dauke da giwaye 45,000, kuma yana fama da tsananin rashin ruwa duk da manyan rijiyoyi da aka gina masu amfani da hasken rana da ke samar da ruwa.

Mahukuntan gandun dajin sun dade suna gargadi game da karancin ruwan sha, wanda ke haifar da karancin ruwan sha da kuma abincin da dabbonin zasu ci, sakamakon yadda kasa ta bushe.

Ko a watan Satumban da ya gabata, hukumar da ke kula da manyan dabbobi ta Zimbabwe ta sanar da cewa karancin ruwa na tilastawa manyan dabbobi yin hijira zuwa yankunan kan iyakar Botswana don neman ruwa da abinci.

Da alama dai wannan matsala ta dade tana ciwa Zimbabwe tuwo a kwarya, don kuwa ko a shekarar 2019 sai da aka bada sanarwa mutuwar giwaye 200, a kudancin kasar duk a saboda rashin ruwa.

Kididdiga ta nuna cewa Zimbabwe tana da giwawe fiye da dubu 100, kuma itace kasa ta biyu da ta fi kowacce yawan giwaye a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.