Isa ga babban shafi

Yau ne za'a gudanar da taron bada kyautar gwarzon dan wasa na Africa

Yau ne ake sar ana gudanar da gagarumin taron bada lambobin girmamawa ga ‘yan wasa da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Africa CAF ke shiryawa, inda taron na bana zai gudana a birnin Marakesh na Morocco.

Za'a gudanar da taron bada kyaututtukan a birnin Marakech na Morocco
Za'a gudanar da taron bada kyaututtukan a birnin Marakech na Morocco AFP - -
Talla

Dan wasan kungiyar Super Eagles ta Najeriya Victor Osimhen zai kara da Muhammad Salah na Masar da kuma Achraf Hakimi na Morocco wajen neman kyautar gwarzon shekara.

Matukar Victor Osimhen ya samu nasarar karbe wannan kambu, zai zama dan Najeriya na farko da ya sami wannan dama tun 1999 lokacin da tsohon dan wasa Kanu Nwankwo ya kai nasarar gida.

Sauran ‘yan wasan Najeriya da suka taba lashe wannan kyauta sun hadar da Rashidi Yekini, da Emmanuel Amuneke da Victor Ikpeba.

Sai dai kuma cikin ‘yan wasan Najeriya kakaf Nwankwo Kanu ne kadai ya kafa tarihin lashe kyautar har sau biyu a shekaru 1996 da kuma 1999.

Masu sharhi kan wasanni dai na ganin watakila Victor mai shekaru 24 ya kafa tarihin karbar kyautar shima, la’akari da irin rawar da yake takawam don kuwa ko a baya-bayan nan shine ya karbe kyautar gwarzon dan wasa na kasar Italiya.

Osimhen ya samu nasarar lashe kyautar takalmin zinare a 2015, bayan kammala gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17, yayin da ya shige cikin jerin mutanen da suka chanchanci karbar kyautar Ballon d’Or inda ya zo na 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.