Isa ga babban shafi

Gwamnatin Ghana ta amince ta karawa ma'aikata albashin da yawansa ya kai kashi 23

Afirka – Gwamnatin kasar Ghana ta amince ta kara yawan albashin ma’aikata da kashi 23 a cikin 100 ga kowanne ma’aikacin dake kasar daga watan Janairu zuwa Yunin shekarar 2024.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo AP - Jacquelyn Martin
Talla

Wata sanarwar hadin gwuiwa tsakanin gwamnatin da wakilan kungiyar kwadagon kasar tace, daga watan Yulin shekarar 2024 zuwa Disamba za’a kuma kara yawan albashin da kashi 25 cikin 100 domin saukakawa ma’aikatan kuncin rayuwar da suka shiga.

Ministan kudin kasar Ken Ofori-Atta yace shaidawa majalisar dokoki cewar tatatlin arzikin Ghana na farfadowa, abinda ke nuna raguwar gibin kasafin kudin da aka gani a cikin wannan shekara da kuma ci gaban da aka gani.

Wata ma'aikaciya a gonar koko dake kauyen Bringakro
Wata ma'aikaciya a gonar koko dake kauyen Bringakro © Sia Kambou / AFP

Kasar Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka ta Yamma dake fama da koma bayan tattalin arziki mafi muni, abinda ya shafi darajar kudin kasar na cedi, da kuma tilastawa gwamnatin karbo rance daga hukumar bada lamuni ta duniya bara, ganin yadda hukumomin kudaden duniya suka juya mata baya.

Ofori-Atta ya shaidawa majalisar dokokin cewar Ghana ta fuskanci kashi 3 gibin kasafin kudi tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, sabanin hasashen da aka yi na sama da kashi 4 da rabi.

Babban bankin kasar ya sayi zinaren da kudinsa ya kai dala biliyan guda domin bunkasa asusun ajiyarsa na kasashen ketare.

Ghana na daga cikin kasashen Afirka dake da arzikin man fetur da koko da kuma zinare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.