Isa ga babban shafi

Ambaliya ta tilastawa sama da mutum 4000 ficewa daga gidajensu a kasar Ghana

Sama da mazauna yankin kudu maso gabashin Ghana 4,000 ne aka tilastawa barin gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa.

Hukumomin kasar sun ce ambaliyar barazana ce ga musamman mazauna kusa da kogunan da suka tumbatsa.
Hukumomin kasar sun ce ambaliyar barazana ce ga musamman mazauna kusa da kogunan da suka tumbatsa. © AP
Talla

Wannan matsala dai ta samo asali ne sakamakon ambaliya da madatsar ruwa ta Akosombo ta haifar, wanda ya yi sanadiyar lalata gidaje da gonaki da ke gabar kogin Volta.

Ambaliyar ta haifar da katsewar ayyuka masu muhimmanci, inda wasu yankunan suka rasa ruwan sha da wutar lantarki.

Gwamnatin Ghana, a cikin wata sanarwa ta fitar, ta tabbatar da cewa dubban mutane a akalla gundumomi tara ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ta kai tsaye, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Hukumar Kula da Bala'i ta Duniya da ke karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya, ta ba da rahoton cewa an samu asarar kayayyaki da kuma ababen more rayuwa a kauyuka bakwai.

Kafin ambaliyar ruwan, hukumar kula da kogin Volta ta ba da shawarwari inda ta bukaci mazauna yankin da su koma wani wuri na daban.

Wannan gargadi ya zo ne sakamakon tumbatsa da madatsar ruwa ta Akosombo ta yi, wanda hakan na da nasaba ne da mamakon ruwan sama da aka dauki sa’o’I ana tafkawa a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.