Isa ga babban shafi

Hatsarin kwale-kwale ya kashe dalibai 9 a kasar Ghana

An tabbatar da mutuwar dalibai tara a yankin Greater Accra na Ghana bayan da wani kwale-kwale da ke dauke da su zuwa makaranta ya kife.

Yadda wani jirgin ruwa ya kife a kasar China
Yadda wani jirgin ruwa ya kife a kasar China © dailytrust
Talla

Rahotanni sun ce, daliban sun taso ne daga Faana zuwa Kelee a karamar hukumar Ga ta Kudu da ke yankin Greater Accra, kuma sun kasance tsakanin shekaru 8 zuwa 15 da haihuwa.

Tuni aka mika gawarwakin yaran takwas daga cikin yaran da aka gano zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na Korle.

A safiyar ranar Alhamis ne aka dauko gawar yaro na 9 bayan wani bincike da matasa suka yi a kogin.

Daraktan Hukumar Kula da ibtila’i ta Kasar Christian Afianyo, ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa yara uku ne suka tsira da rayukansu.

Ya ce wani yaro daya daga cikin daliban yana aikin kwale-kwalen kafin faruwar lamarin duk da cewa bai da tabbas kan wannan labarin.

Mista Afianyo ya ce watakila yaron yana daya daga cikin mutane ukun da suka tsira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.