Isa ga babban shafi

Ghana za ta fara amfani da maganin Malaria na Jami'ar Oxford

Gwamnatin Ghana ta amince a fara amfani da wani sabon maganin zazzabin cizon sauro kan yara a kasar. Wannan na zuwa ne bayan da a karon farko maganin wanda jami’ar Oxford ta Birtaniya ta samar, ya samu amincewar mahukunta wajen yin amfani da shi ko'ina a duniya. 

Cutar Malaria ta fi kamari a kasashen Afrika
Cutar Malaria ta fi kamari a kasashen Afrika © Shutterstock/mycteria
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, jami’ar ta Oxford ta ce, za a rika amfani da allurar rigakafin kamuwa da zazzabin na Malaria ne akan yara ‘yan watanni 5 zuwa 36, wadanda dama su ne binciken kimiyya ya bayyana cewar sun fi fuskantar hatsarin mutuwa saboda cutar. 

Farfesa Adrian Hill, da ya jagoranci aikin harhada rigakafin na R21/Matrix-M, ya ce sai da aka shafe shekaru 30 ana gudanar da bincike kafin samar da shi, kuma ya zarce sauran magungunan zazzabin Malaria inganci, wanda za a rabawa kasashen Afirka da suka fi bukatarsa. 

Tawagar kwararru na kasa da kasa da suka gudanar da binciken samar da allurar rigakafin, sun bayyana fatan cewar zai karfafa yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro, wanda kididdiga ta nuna ya kashe mutane akalla 627,000 a fadin duniya, akasarinsu yara daga nahiyar Afirka a cikin shekarar 2020 kadai. 

A shekarar da ta gabata, wata allurar rigakafin ta daban da kamfanin harhada magunguna na Birtaniya GSK ya samar, ta zama na farko da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ba da shawarar yin amfani da ita, allurar da  tuni  aka yi wa yara sama da miliyan guda a Afirka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.