Isa ga babban shafi

Daruruwan mutane sun rasa matsuguni a Ghana sakamakon ambaliya

Ambaliyar ruwa ta mamaye daruruwan gidaje a kusa da madatsar ruwan Weija dake kasar Ghana, abinda ya kaiga lalata tarin dukiyar da ya kai miliyoyin Cedi a cikin kasar.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankuna
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankuna © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ko da yake ba’a sanar da rasa rayuka ba, ambaliyar tayi sanadiyar lalata motoci da gidaje da kayan aikin gida da kuma kadarori da dama da jama’a suka mallaka.

Bayanai sun ce bude ruwan da Hukumar kula da ruwa tayi daga Madatsar ruwan Weiji domin hana shi fashewa ya haifar da ambaliyar.

Daga cikin yankunan da aka samu ambaliyar akwai Oblogo da Tetegu da New Weija da SCC da Tatop da ‘Sampa Valley’ da kuma wasu sassan ‘Top Town’ da ‘American Farm’ a Ngleshie Amanfro.

Rahotanni sun ce wadannan yankunan da ambaliyar ta shafa ciki harda madatsar ruwan Weija na daga cikin wuraren yawon bude ido da baki ke ziyara.

Hukumar kula da ruwar Ghana tace irin halin da Madatsar ruwan ta samu kanta, ya tilasta musu bude hanyoyi guda 4 domin rage ruwan da kuma hana shi fashewa.

Babban jami’in yada labaran Hukumar, Stanley Martey yace ya zuwa wannan lokaci Madatsar ruwan na da zurfin kafa 49 da rabi, sabanin kafa 48 da ake bukata, yayin da ake bukatar rage ruwan da zaran yawansa ya kai kafa 46 da rabi domin kare shi.

Martey yace duk da yake basu bada sanarwa ba kafin bude ruwan, tun daga watan Afrilu suke gargadin jama’a dangane da barazanar da suke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.