Ana fargabar barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya
A daidai wannan lokaci da manoma suka fara girbe amfanin gona a mafi yawan yanku a Najeriya, wani abu da ake fargaba shi ne samun faruwar rikici tsakanin manoma da makiya.
Wallafawa ranar:
Shugabannin al’ummomin biyu dai sun ce suna iya kokarinsu domin kauce wa rikice-rikice da wasu lokuta ke haddasa asarar rayuka.
Fulani galibinsu makiyaya ne da ke zaune a Yammacin Afirka, kuma rayuwarsu ta dogara ne da kiwon shanu, da kuma awaki da tumaki.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Ahmed Alhassan.
Rahoto kan rikicin manoma da makiyaya a Najeriya
A cikin 'yan shekarun nan, yayin da canjin yanayi ya kawo karuwar kwararowar hamada da karancin albarkatu, rikice-rikicen Fulani da manoma sun yawaita.
Rikicin manoma da makiyaya
Yayin da ake samun rikice-rikicen makiyaya da manoma a Najeriya, ana danganta rikicin Fulani da manoma da tsattsauran ra'ayi saboda ana zargin su da amfani da ta’addanci da tashin hankali a matsayin dabarun cinye amfanin gona.
A wasu sassan Afirka, kamar Mali, an kafa kungiyoyin 'yan ta'adda, kamar Front de Libération du Macina (FLM) da ta kasance mai shiga tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Duk da yake a halin yanzu babu wata kungiya a Najeriya, da aka sani a matsayin mai shiga tsakanin manoma da makiyaya, ana ganin Fulani sun sauya salon haifar da tashe-tashen hankula, ta hanyar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, inda a wasu yankunan ma su na hana manoma shuka ko kuma girbe amfanin gona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu