Isa ga babban shafi

Tan dubu 34 na takin Najeriya ya makale a iyakokin Turai - Lavrov

Gwamnatin Rasha ta ce akwai tan dubu 34 na takin zamani da ta aiko wa Najeriya, sai dai kuma sun makale a gabar ruwan Turai.

Sergei ya ce bai kamata rikicin da ke tsakanin kasar da Ukraine ya shaffi kasashen da basu ji ba basu gani ba
Sergei ya ce bai kamata rikicin da ke tsakanin kasar da Ukraine ya shaffi kasashen da basu ji ba basu gani ba AP - Mary Altaffer
Talla

Da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran kasar Rasha, ministan harkokin wajen kasar Sergie Lavrov a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai takin zamani fiye da tan dubu 260 da  Rasha ta baiwa wasu kasashen duniya amma suke makale a iyakokin kasashen Turai.  

A cewar sa, duk wannan takin kyauta ne kasar za ta baiwa kasashen Africa da suka hadar da Malawi, Kenya da kuma Najeriya, amma batun rashin jituwar da ke tsakanin kasar da kasashen Turai ne dakile wannan yunkuri.

Tan dubu 34 na takin zamanin dai-dai yake da buhu dubu 680.

Tun bayan kaddamar da farmakin da Rasha ta yi a Ukraine, kasar ke fuskantar takunkumi daban daban, ciki harda dakatar da ita wajen fitar da kayayyakin da take sarrafawa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.