Isa ga babban shafi

Dan kunar bakin wake ya tayar da bama-bamai a Somalia

A Somalia ma'aikatan agajin gaggawa na ci gaba da gano gawarwakin mutane a karkashin baraguzan gine- bayan da wani dan kunar bakin wake ya  tayar da wata motar daukar kaya.

Wani  hari bam da mayakan Al Shabaa ta kai a birnin Mogadishu a watan Oktoban shekarar 2022.
Wani hari bam da mayakan Al Shabaa ta kai a birnin Mogadishu a watan Oktoban shekarar 2022. ABDIHALIM BASHIR via REUTERS - ABDIHALIM BASHIR
Talla

Harin da dan kunar bakin wake ya kai a kan wani shingen binciken jami’an tsaro a garin Beledweyne a jiya Asabar, lamarin da ya haifar da fashewar bam da ya sa mutane da dama suka makale a karkashin bulo da siminti.

'Yan sanda sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa adadin wadanda suka mutu ya haura mutane 13 da aka ruwaito tun farko amma ba su iya bayar da takamaiman adadi ba.

Mataimakin kwamandan ‘yan sandan Beledweyne Sayid Ali ya ce, "Ana gudanar da bincike don gano gawarwaki a wurin da fashewar ta afku a safiyar yau a karkashin baraguzan gine-gine."

Harin dan kunar bakin wake a Somalia
Harin dan kunar bakin wake a Somalia © AP

 

Jami’in ya bayyana cewa  dan kunar bakin waken ya auna wata unguwa mai cike da hada-hadar jama’a da ke dauke da kasuwa da gine-gine. Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana alhininsa yan lokuta bayan wannan harin, inda ya ninka alkawarinsa na "kawar da" 'yan ta'addar Al-Shabaab da suka yi ta tayar da kayar baya ga gwamnatin tsakiyar kasar mai rauni sama da shekaru 15.

Wani jami’in ‘yan sandan yankin Ahmed Yare Adan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa a jiya cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 tare da jikkata 45. Mataimakin ministan kiwon lafiya na Somaliya Mohamed Hassan ya fada a yammacin jiya Asabar cewa "kusan mutane 13 da suka samu munanan raunuka, an kwashe su daga Beledweyne a cikin daren kuma an kai su Mogadishu babban birnin kasar domin yi musu magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.