Isa ga babban shafi

Mayakan Al-Shabaab sun kashe mutane 5 a wasu hare-haren da su kai Kenya

Mayakan Al-Shabaab sun kashe fararen hula 5, ta hanyar fillewa wasu kai a gabashin Kenya, kamar yadda shedun gani da ido da kuma jami’an ‘yan sanda suka tabbatar.

Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia
Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia RFI-Swahili
Talla

‘Yan sanda sun ce a cikin daren Asabar ne aka kai harin kan kauyukan Juhudi da Salama da ke Lamu, kan iyakarta da Somaliya.

Hassan Abdul, wanda ya shaida faruwar lamarin, ya ce kimanin maharan da ke dauke da bindigu da kuma wukake 20 zuwa 30 ne suka kai harin, inda suka rufe mata biyu a cikin gida sannan suka fitar da mazan waje, su ka daure su kuma suka yi musu kisan gilla ta hanyar yankewa wasu harshe wasu kuma fille ma wasu kai.

A cewar wani mazaunin yankin Ismail Hussein, maharan sun kuma kwashi kayan abinci da sauran kayayyaki, kafin su bar ganin suna harbin iska.

Al-Shabaab da ke da alaka da Al-Qaeda, ta fidda wata sanarwar da ke ikarin cewar takai hari Juhudi, inda ta kashe mutane 6 ta re da kona gidajen mabiya addinin Kirista 10 a Kenya.

Sama da shekaru 15 ke nan, Al-Shabaab ke yaki da gwamnatin Somaliya da ke samun goyon bayan kasashen waje.

Haka nan ta sha kai munanan hare-hare cikin Kenya, ina a wasu da ta kai a shekarar 2013 ta kashe mutane 67 na shekarar 2015 mutane 148 ne suka mutu, sai kuma na watan Janairun 2019 inda mutane 21 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.