Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 12 sun mutu sakamakon harin Alshabab a Mogadishiu

Hukumomi a kasar Somalia sun tabbatar da mutuwar mutane 12, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a wani hotel da ‘yan majalisar dokokin kasar ke zaune a birnin Mogadishiu.

Harabar fadar shugaban kasar Somalia
Harabar fadar shugaban kasar Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce a sanyin safiyar yau ne ‘yan bindigar suka afka wa wannan hotel, yayin da wasu majiyoyi ke cewa da farko wata mota ce da aka dana bam ta tashi a harabar wannan hotel kafin a fara buda wuta.

Tuni dai jami'an wanzar da tsaro da zaman lafiya na Tarayyar Afirka suka kwace iko da wannan otel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.