Isa ga babban shafi
Somaliya

An kashe dakarun wanzar da zaman lafiya 50 a Somalia

Mayakan Al Shebab sun kashe Sojoji akalla 50 a harin da suka kai sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika a kudancin Somalia.An kai harin ne a jiya Talata, wanda aka bayyana hari mafi muni da mayakan Shebab suka kai kan sojojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia.

Gawarwakin dakarun wanzar da zaman lafiya na AMISOM a Somalia da al-Shabaab suka kaiwa hari
Gawarwakin dakarun wanzar da zaman lafiya na AMISOM a Somalia da al-Shabaab suka kaiwa hari Reuters/路透社
Talla

Mayakan na al Shebab sun kai harin ne a sansanin sojin Afrika a garin Janale da ke nisan kilomita 80 da Mogadishu babban birnin kasar Somalia.

Kuma akalla dakarun wanzar da zaman lafiya 50 aka kashe a harin wanda aka bayyana mafi muni da aka kai wa dakarun na Afrika.

Kuma rahotanni sun ce kimanin sojoji 50 suka bata.

Mayakan na al shebab sun ce sun kai harin ne domin daukar fansan kisan wasu fararen hula da dakarun Uganda suka yi a wajen daurin auren a garin Merka.

Cikin Sojojin na rundunar Afrika a Somalia da aka kashe sun hada da na Hasbaha da Kenya da Burundix da Djobouti.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar Amison tace t ana kan tantance girman harin da kuma adadin wadanda aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.