Isa ga babban shafi
Somaliya-MDD

Barazanar yunwa a kasar Somalia ta ta'azara

Majalisar dinkin duniya ta nuna damurta tare da gargadi kan halin da Kasar Somalia ke sake fadawa na matsananciyar yunwa, sama da shekaru 4, ba tare da samun mafita ba.

Wani yaro dake fama da matsananciyar yunwa a kasar Somalia
Wani yaro dake fama da matsananciyar yunwa a kasar Somalia
Talla

Majalisar ta bayyana fargabar ta, kan karuwar alkallumar kasar da ke cikin bukatar abinci cikin gaggawa.

Rashin abinci da yunwa na sake ta’azara sama da yadda ake tsamani a Somalia, duk da irin kokarin da kungiyoyin jin kai, da na masu bada taimako ke yi wajen kare ‘yan kasar daga barazanar ta yunwa.

Jami’in Majalisar na dinkin duniya a kasar, Peter de Clercq ya ce matsalar tafi kamari tsakanin mutane da yaki ya tagayara, inda ya kara da cewa, an samu karuwar kaso 17 cikin 10 sama da watanni 6 baya, adadin da ya sanya ake da mutane 855,000 daga 731 da ke neman abin kaiwa baka a cikin watannin baya.

Yayyin da ake da kanana yaran ‘yan kasa da shekaru 5, dubu 215 da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, wanda a halin yanzu dubu 40 ke fama da tsananin cututtuka da ka iya sanadi ran su.

Har yanzu rashin zaman lafiya ya gagara samuwa a Somalia inda mayakan al-Shebab, da ke da alaka da al-Qaeda ke cigaba da gwabza rikici da dakarun gwamnati.

A shekarar 2011 sama da mutane dubu 250 yunwa ta kashe a kasar Somalia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.