Isa ga babban shafi

Morocco ta ware kusan dala biliyan 12 don sake gina yankunan da aka yi girgizar kasa

Gwamnatin Morocco ta sanar  da ware dirham biliyan 120, kwatankwacin sama da dala biliyan 11 don sake gina yankunan da aka yi  mummunar girgizar kasar. 

A ranar 8 ga watan Satumba ce girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8 ta addabi Morocco.
A ranar 8 ga watan Satumba ce girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8 ta addabi Morocco. REUTERS - NACHO DOCE
Talla

A wata sanarwa, gwamnatin ta ce ta ware kudaden ne don gudanar da aikin taimaka wa mutane miliyan 4  da dubu dari 2 da wannan girgizar kasa ta shafa a cikin shekaru 5 masu zuwa. 

A ranar  8 ga watan Satumba ce girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8 ta afkawa lardin Al-Haouz da ke kudancin Marrakesh, inda ta yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 3 tare da jikkata dubbai. 

Girgizar kasar ta lalata dubban gidaje a  yankin tsakiyar Morocco, ciki, abin da ya  tilasta wa iyalai da dama kwana a waje cikin sanyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.