Isa ga babban shafi

Morocco ta kama hanyar amincewa da taimakon kasa-da-kasa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani lokaci daga yanzu kasar Maroko na iya sanar da bukatar neman agaji kasashen duniya domin taimaka mata farfadowa daga mummunar girgizar kasar da ta kashe kusan mutane 3,000 tare da lalata dubban gidaje. 

Wasu daga cikin kayan agaji da suka isa yankin Marrakech na kasar Morocco da girgizar kasa ta yi barna. 13/09/23
Wasu daga cikin kayan agaji da suka isa yankin Marrakech na kasar Morocco da girgizar kasa ta yi barna. 13/09/23 AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Shugaban jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Geneva, ya ce suna da kyakkyawar fata cewar Morocco zata sassautan matsayinta wajen amincewa taimakon kasa-da-kasa ya isa zuwa kasar tsakanin yau ko gobe. 

Griffiths wanda ya ce ya tattauna da mahukuntan Morocco kan wannan batu, ya bayyana shirinsu na jagorantar ayyukan jinkai a kasar, wajen samar da matsugunai ga wadanda suka tsira daga iftila’in da kuma  abinci da kayayyakin kiwon lafiya. 

Kin amincewa da wasu kasashe

Ya zuwa yanzu, Kasar Morocco ta baiwa kungiyoyin agaji daga kasashen Spain da Burtaniya da Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa ne kadai izinin shiga kasar tun bayan girgizar kasar mai karfin kusan maki 7 da ta afka mata ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta yi watsi da tayin wasu kasashe da suka hada da Amurka da Faransa da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya. 

Alhamis din nan ne kasar Morocco ta sanar da kaddamar da wani shirin tallafawa wadanda lamarin ya shafa, wajen tsugunar da mazauna kusan gidaje dubu 50 da suka ruguje, tare da umarnin kai agajin gaggawa da kudin su ya kai dirhami dubu 30 (kusan dalar Amurka 3,000) ga magidantan da abin ya shafa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.