Isa ga babban shafi

Babu bukatar jayayya tsakanin Faransa da Morocco kan agaji- Macron

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa, babu bukatar muhawar kan matakin Morocco na kin karbar agajin kasar duk da halin da ta shiga biyo bayan girgizar kasar da ta kashe mutanen da yawansu ya tasamma dubu 3.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - TERESA SUAREZ
Talla

A jawabin da ya gabatar ta cikin wani sakon bidiyo, cikin daren jiya talata, bayan Morocco ta sake nanata rashin bukatarta ga tallafin na Faransa, Macron ya ce kasar ba ta bukatar doguwar tattaunawa ko jayayya lura da bukatar da ta ke da shi a halin da ake ciki.

Ana dai alakanta matakin na Morocco da yadda Faransa ke karfafa alakarta da Algeria wanda ya kai ga dakatar da ziyarar da Macron ke shirin kai wa kasar tsawon lokaci.

A shekarar 2021 ne Algeria ta katse duk wata Hulda da ke tsakaninta da makwabciyarta Morocco bayan zarginta da kai mata hari, lamarin da ya kai ga kulle iyakokin kasashen biyu ga juna.

A cewar Macron zabi ya rage ga Sarki Mohammed na 6 da gwamnatin Morocco zu ware kasashen da za su karbi agajinsu, sai dai akwai fatan dukkanin muhawara da rarrabuwar kan da aka samu tsakanin kasashen biyu ya kawo karshe don tunkarar halin da ake ciki.

Zuwa yanzu dai Morocco ta karbi agaji daga kasashen Spain da Birtaniya da Qatar da kuma hadaddiyar daular larabawa amma ta yi watsi da tallafin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.