Isa ga babban shafi

Masu aikin ceto daga kasashen duniya sun isa Morocco

Har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman mutanen da gine-gine suka danne a sakamakon girgizar kasar Morocco, sa’o’i 48 bayan faruwar ta.

Girgizar kasar ta raba dubban mutane da muhallansu, lamarin da ya tilasta musu samun mafaka a cikin tantuna.
Girgizar kasar ta raba dubban mutane da muhallansu, lamarin da ya tilasta musu samun mafaka a cikin tantuna. REUTERS - HANNAH MCKAY
Talla

Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane sama da 2,500 a girgizar kasar da ba’a taba ganin mai karfin ta ba tun shekaru 150 da suka gabata a kasar.

Tawagar masu aikin ceto daga kasashen Spaniya, Burtaniya da kuma Qatar tuni suka hallara don taimakawa takwarorin su na Morocco, a dai-dai lokacin da ake fargabar da wuya a kara samo masu rai a kasa, saboda yadda lokaci ke dada yin nisa.

Bayanai sun ce wadanda suka tsira daga girgizar kasar sun shafe kwanaki uku yanzu haka a waje, saboda yadda girgizar kasar ta lalata gidajen su.

Faya-fayan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda mata da kananan yara ke samun mafaka a tantunan wucin gadi da aka kafa a filin Allah ta’ala, yayin da maza ke rayuwa ba tare da tantin ba.

Sai dai jama’a a kasar na ci gaba da kokawa kan yadda ceton ke tafiyar wahaininya, kamar yadda Hamid Ben Henna mazaunin kauyen Tafeghaghte, na gabashin kasar da ya rasa dansa mai shekaru 8, ya ce har kawo yanzu ba’a kai ga ceto dan sa mai shekaru 3 da gini ya danne ba, a don haka suna cikin fargaba da rashin tabbas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.