Isa ga babban shafi

Girgizar kasa: Za a yi makokin kwanaki 3 a Morocco bayan mutuwar mutane sama da 2000

Sarkin Morocco, Mohamed Na Shida ya ayyana kwanaki 3 na makoki a fadin kasar don juyayin wadanda kakkarfar  girgizar kasa da aka yi a kasar ranar  Juma’a ta  rutsa da su.

King Mohamed VI, Sarkin Morocco.
King Mohamed VI, Sarkin Morocco. AFP PHOTO/FADEL SENNA
Talla

Wata sanarwa daga masarautar Morocco ta ce za a saukar da tutar kasar kasa-kasa a dukkannin gine-ginen gwamnati a ilahirin kwanakin da za a shafe ana makokin.

Sarkin na Morocco ya kuma yi umurnin kafa wani kwamiti  na ministoci da zai tsara shirin sake gina gidajen da suka lalace sakamakon wannan girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8.

Sama da mutane dubu 2 ne suka mutu, a yayin da fiye da dubu 1 suka jikkata sakamakon wannan girgizar kasa da ta auku ranar Juma’a.

Wadanda suka mutu sakamakon wannan girgiszar kasa suna yankuna dabam-dabam ne da suka hada  da Al Haouz da Marrakesh, da kuma biranen Ouarzazate, Azilal, Chichaoua, da Taroudant, kamar yadda wata  sanarwa daga ma’aikatar cikin gidan kasar ta  bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.