Isa ga babban shafi

Adadin mamata sakamakon girgizar kasar Morocco ya zarta 2,800

Kwarin gwiwar samo karin mutane a karkashin baraguzai sakamakon girgizar kasar Morocco na ci gaba da ja baya, yayin da adadin mamata ya kai 2,800.

Gine-ginen kasa da suka kwabe zuwa laka, ne dlilin da ke haddasa tafiyar wahainiya a aikin ceto
Gine-ginen kasa da suka kwabe zuwa laka, ne dlilin da ke haddasa tafiyar wahainiya a aikin ceto AFP - FADEL SENNA
Talla

Wannan itace girgizar kasa mafi muni da kasar ta taba gani a tarihin ta, la’akari da yawan mutanen da suka mutu da kuma dubbai da suka jikkata.

Sa’o’i 48 bayan faruwar ta, ana fargabar samun masu rai a karkashin kasa zai yi wuya, duba da yadda aikin ceton ke tafiyar wahainiya.

Kafar talabijin din kasar ta tabbatar da mutuwar mutane 2,862, sai wasu 2,562 da suka gamu da munanan raunuka.

Masu aikin ceto na kasashen duniya da suka isa kasar sun koka da yadda laka ke hana aikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.