Isa ga babban shafi

Faransa ta roki Morocco kan ta karbi tallafin da ta ke so ta bata

Gwamnatin Faransa ta roki kasar Morocco kan ta daure ta karbi tallafin da take yunkurin bata, a dai-dai lokacin da adadin mamata sakamakon girgizar kasa ya zarce dubu 3.

Macron ya ce ya kamata Morocco ta gane cewa wannan lokaci ne da take bukatar taimako ba wai duba masalahar siyasa ba.
Macron ya ce ya kamata Morocco ta gane cewa wannan lokaci ne da take bukatar taimako ba wai duba masalahar siyasa ba. © Geert Vanden Wijngaert/AP
Talla

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce akwai bukatar Morocco ta manta da tsamin alaka da ke tsakanin su saboda dalili na siyasa ta duba halin da talakawa ke ciki, tare da karbar tallafin da Faransar ke shirin bata.

Ta cikin wani dogon jawabi da ya wallafa a shafin sa na X Emmanuel Macron yace gwamnatinsa na tare da Morocco ko yau ko gobe, kuma a shirye take ta bata tallafi a duk lokacin da ta bukata.

Tun bayan faruwar girgizar kasa ta daren Juma’a, gwamnatin Paris ta ware yuro miliyan biyar da nufin kaiwa kasar Morocco tallafi, sai dai kuma a wani abu mai kama da watsa kasa a ido Moroccon ta ce bata bukatar tallafi daga Faransa.

Alaka dai ta yi tsami a tsakanin Morocco da Faransa tun bayan da ita Faransar ta ke kara kusantar Algeria, kasar da ke makwaftaka da Morocco amma kuma ba’a ga maciji.

Haka kuma Moroccon na ganin baiken Faransa kan kin goyon bayan yankin Western Sahara kamar yadda kasashen Amurka da Isra’ila suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.