Isa ga babban shafi

Bakin-haure dari 4 na daga cikin wadanda suka mutu a ambaliyar Libya

Wani rahoton Hukumar kula da aikin agaji ta Majalisar Dinkin Duniya  ta ce kimanin bakin haure 400 ne suka mutu sakamakon ambaliyar da ta addabi gabashin kasar Libya.

Masu aikin agaji a yankin Derna,wanda ya fuskanci ambaliya.
Masu aikin agaji a yankin Derna,wanda ya fuskanci ambaliya. AP - Yousef Murad
Talla

Rahoton ya ruwaito Hukumar Lafiya ta Duniya na cewa kimanin mutane dubu 4 ne  suka mutu a ambaliyar ruwan, adadin da ya kunshi bakin-hauren da ke zaune a yankunan da lamarin ya auku.

Dubban bakin haure daga Afrika da Gabas ta Tsakiya ne ke zaman wucin gadi a Libya, kuma da daman su ne ke daukar kasadar tafiya mai hatsari zuwa Turai ta tekun  Mediterranean.

Tun da farko Hukmar Kula da Bakin-Haure ta Majalisar  Dinkin Duniya ta ce akwai kimanin bakin-haure dubu 100 a wannan yanki na kasar Libya da ambaliyar ruwa ta yi ta’adi na gabashin  Libya, cikinsu har da sama da dubu 8 a birnin Derna; kuma akasarin su sun fito ne daga kasashen Chadi, Sudan da Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.