Isa ga babban shafi

'Yan ci rani 35 sun mutu a gabar ruwan Libya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 35 ‘yan ci rani ake kyautata zaton sun mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife a gabar tekun Libiya.

Jami'an agaji na kasar Jamus yayin aikin ceton 'yan ci rani daga nutsewa cikin teku.
Jami'an agaji na kasar Jamus yayin aikin ceton 'yan ci rani daga nutsewa cikin teku. © Selene Magnolia/Sea-Watch/Handout via REUTERS
Talla

Hukumar ta IOM ta ce jirgin ruwan ya nutse ne a yammacin birnin Sabratha na kasar Libya, inda daga nan ‘yan ci rani daga Afirka ke kaddamar da balaguro mai hatsarin gaske na kokarin tsallaka tekun Mediterrenean.

IOM ta ce an tsamo gawarwakin mutane shida daga cikin tekun yayin da 29 suka bace, wadanda ake kyautata zaton sun mutu. Har yanzu kuma ba a bayyana dalilin da ya sa jirgin ruwan da suke ciki na katako ya kife ba a ranar Juma'ar da ta gabata.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM, ta ce a cikin makon da ya gabata kadai, akalla mutane 53 suka mutu, ko kuma ake zaton sun mutu a gabar tekun Libiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.