Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun hallaka sojojin Burkina Faso 53

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sanar da mutuwar sojojinta 17 da wasu jami’an sa-kai 36 a wata gagarumar arangama tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro.

Baya ga sojojin da aka kashe akwai karin wasu da daga da suka bata
Baya ga sojojin da aka kashe akwai karin wasu da daga da suka bata AFP via Getty Images - AHMED OUOBA
Talla

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar tace ‘yan ta’addar sun farwa sojojin ne a kauyen Yatenga, inda sojojin ke aikin tabbatar da tsaro kuma ba tare da bata lokaci ba suka bude musu wuta.

Sanarwar ta kuma kara da cewa duk da sojojin sun mayar da martani, amma kuma wutar ta yi tsananin da sai da ‘yan ta’addar suka hallaka sojojin 17.

Burkina Faso ta kasance cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan ta’adda tun 2015, lokacin da mambobin kungiyar Al-Qaeeda suka fara kai munanan hare-hare a sassan kasar.

Bayanai sun nuna cewa hare-hare sun tsananta a kasar tun bara, duk kuwa da yadda sojojin ke ikirarin tabbatar da tsaro bayan karbe iko daga hannun farar hula.

Faransa dai ta dade tana gargadin cewa matukar sojojin ta suka fice daga kasar, ayyukan ta’addanci zasu ci gaba da fadada, sai dai duk da haka sojojin sun gwammace sun kulla alaka da wasu kasashen a maimakon ci gaba da alaka da Faransa.

Ko a lokacin da ‘yan kasar ke zanga-zangar nuna goyon bayan su ga sojoji an ga yadda suka rika daga tutar kasar Rasha, da kuma kira kan ta kaiwa kasar dauki ta fannin yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.