Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane 24 a Burkina Faso

Akalla mutane 24 da suka kunshi ‘yan sa-kai da fararen hula ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi suka kashe a Burkina Faso. 

Wasu jami'an tsaron Burkina Faso a shekarar 2018
Wasu jami'an tsaron Burkina Faso a shekarar 2018 AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Wasu mazauna yankin da suka tabbatar da aukuwar lamarin sun ce ‘yan ta’addan sun kai  harin kan kauyen Bittou wanda ke kusa da iyakar kasashen Ghana da Togo, inda suka halaka ‘yan sa-kai 20 da kuma wasu fararen hula 4. 

Wasu majiyoyi sun kuma ruwaito da cewar, akwai wasu mutanen da dama da suka bace bayan farmakin na ranar Talata. 

Wata kididdiga da kungiyoyin farar hula suka fitar a Burkina Faso ta nuna cewar, kawo yanzu hare-haren ‘yan ta’addda yayi sanadin mutuwar mutanne fiye da dubu goma, tare da raba wasu fiye da miliyan biyu da muhallansu. 

A baya bayan nan shugabban gwanatin sojin Burkina Kaftin Ibrahim Traore ya sha alwashin kwato kashi 40 na kasar da a yanzu ke karkashin ikon mayakan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.