Isa ga babban shafi

'Yan ta'addda sun kashe jami'an tsaro 42 a Burkina Faso

Sojoji 10 da wasu fararen hula 'yan sa-kai 32 da ke taimaka wa dakarun Burkina Faso ne aka kashe a ranakun asabar da lahadi a wasu hare-hare biyu da aka kai a arewacin kasar, wadanda a cikin wannan mako suka ba da umarnin gani an kawo karshen tashe-tashen hankulan masu da'awar jihadi.

Shugaban majalisar Sojin Burkina Faso Kyaftin  Ibrahima Traoré
Shugaban majalisar Sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahima Traoré AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Sojojin sun tabbatar da cewa mayaƙa arba'in" sun mutu ("sojoji takwas da VDP talatin da biyu") kuma sun kara da cewa "aƙalla 'yan ta'adda 50" sun fuskanci mayar da martani daga sojojin saman kasar ta Burkina Faso.

Gwamnan yankin Arewa ya nuna a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa mutane 33 suka jikkata" a harin na farko aka kuma garzaya da su asibitin Jami'ar yanki na Ouahigouya, babban birnin yankin Arewa. Sojojin sun rubuta cewa "wasu biyu da suka jikkata" a harin na biyu an kuma kwashe su zuwa asibiti.

Wani mazaunin birnin ya shaida cewa: "hakika an gwabza kazamin fada ranar asabar da maraice" kusan sa'o'i biyu.

Ya kuma yi ikirarin cewa dakarun kasar sun mayar da martani tare da kai "hare-hare da dama ta sama kan wuraren da ake zargin masu jihadi ne" a ranar Juma'a.

Taswirar kasar Burkina Faso
Taswirar kasar Burkina Faso © RFI

A ranar Alhamis, hukumomin rikon kwarya a Burkina Faso - wadanda suka hau kan karagar mulki a watan satumba, sun zartar da "tattaunawa na gama-gari" da sheilar cewa duk wani dan kasar mai shekaru 18 doka ta ba shi damar shiga aikin soja, domin tunkarar hare-haren 'yan jihadi da ke addabar kasar.

Rikicin na Burkina Faso ya kashe fiye da mutane 10,000 akasarin su fararen hula da sojoji a cewar kungiyoyi masu zaman kansu, kuma wasu milyan biyu sun rasa matsugunansu.

A watan Fabrairu, shugaban rikon kwarya, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana "yunƙurinsa" na yaƙar masu jihadi, duk da yawaitar hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.