Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane 44 a Burkina Faso

Bayanai daga Burkina Faso na cewa fararen hula 44 sun mutu sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai kan kauyukan Kourakou da Tondobi da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gwamnan yankin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa. 

Sojojin Burkina Faso kan hanyar su na zuwa Ouagadougou.
Sojojin Burkina Faso kan hanyar su na zuwa Ouagadougou. REUTERS/Joe Penney
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar sun kai hari kauyukan ne a tsakar daren ranar Juma'a, inda kuma suka bude wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya hallaka mutane 44. 

A karin bayanin da ya yi, gwamnan lardin Rodolph Sorgho ya ce mutane 31 ne aka kashe a kauyen Kourakou sai wasu 13 da suka mutu a kauyen Todobi. 

Rabon da yankin ya ga irin wannan mummunan harin tun wanda aka kai a watan Yulin bara, wanda ya lakume da rayukan mutane 86. 

Gwamna Rodolph ya ce tuni sojoji suka isa yankin don tabbatar da doka da oda da kuma kwantarwa da mutane hankali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.