Isa ga babban shafi

Gwamnatin Togo ta tsawaita dokar ta baci a arewacin kasar

Majalisar dokokin Togo ta kada kuri'ar tsawaita wa'adin dokar ta baci a yankin Savanes na tsawon watanni 12.

Sojojin Togo kenan yayin wata rakiya da suka yiwa shugaban kasar, Faure Gnassingbe a Arewacin kasar, ranar 16 ga watan Fabrairu, 2020.
Sojojin Togo kenan yayin wata rakiya da suka yiwa shugaban kasar, Faure Gnassingbe a Arewacin kasar, ranar 16 ga watan Fabrairu, 2020. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Hukumomin kasar na da nufin taimakawa wajen hana kutse daga kungiyoyin masu jihadi a kan iyakar kasar da Burkina Faso, wato daga arewacin kasar mai nisa.

An kawo karshen dokar ta bacin a cikin makonnin da suka gabata bayan karin wa’adin farko na watanni shida a watan Satumba.

Shugaba Faure Gnassingbe ne ya zartar da wannan doka tun a watan Yunin 2022.

Dokar ta baci ta ba wa jami'an tsaro da hukumomin yankin damar daukar matakan gaggawa don yakar barazanar kungiyoyin 'yan ta’adda a kasar da ke Yammacin Afirka.

Ministan Tsaron kasar Janar Damehame Yark ya ce "halin da ake ciki abun damuwa ne matuka, musamman a arewa mai nisa na kasar, "bisa la'akari da ci gaba da sabbin yunkurin masu dauke da makamai, duk da cewa jami’an tsaronmu na kokarin tunkarar su, amma muna ganin ya kamata mu dauki wasu sabbin matakan".

Tun daga watan Nuwamban 2021, ake kai hare-hare a arewa mai nisa, kusa da kan iyaka da Burkina Faso, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke iko da sassan kasar.

Hare-hare sun karu a 'yan watannin nan a yankunan kan iyakar kasar Togo, kamar yadda rahotanni daga jaridun kasar suka bayyana.

Sai dai tun daga watan Agustan shekarar 2022, gwamnati ko sojoji ba su yi wani bayani ba game da yanayin tsaro a arewacin kasar.

'Yan adawar Togo da kungiyoyin farar hula sun sha yin tir da halin ko in kula da hukumomin kasar ke nunawa kan sha’anin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.