Wani harin ta'addanci ya hallaka sojojin Burkina Faso da dama
Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso tace akalla sojinta 33 suka gamu da ajalinsu yayin da wasu 12 suka jikkata samakon wani kazamin kari da aka kai wani sansanin sojinta a gabashin kasar ranar Alhamis.
Wallafawa ranar:
Harin da aka kai a safiyar ranar Alhamis ya auna sansanin sojojin da ke Ougarou, a yankin gabashin Burkina Faso.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce sojojin da aka yi wa kawanya sun kashe ‘yan ta’adda akalla 40 kafin a kai musu dauki.
Karuwar hare-hare
Burkina Faso dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da dama da ke fama da tashe tashen hankulan masu kaifin kishin Islama da suka barke daga makwabciyar kasar Mali cikin shekaru goma da suka gabata, inda suka kashe dubban mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu.
Tashe-tashen hankula a kasar sun yi kamari a 'yan watannin da suka gabata yayin da hukumomi ke kokarin dawo da martabar kasar duk da karfafa ayyukan tsaro.
Mutuwar sama da mutane 150
Ko a makon jiya wasu mutane sanye da kayan sojoji sun kashe akalla mutane 150 a wani samame da suka kai a wani kauye da ke arewacin Burkina Faso, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu