Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane 60 a Burkina Faso

Rahotanni daga arewacin Burkina Faso sun ce gungun wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kashe mutane 60 a kauyen Karma da ke lardin Yatenga.

Tasiwirar kasar Burkina Faso
Tasiwirar kasar Burkina Faso © RFI
Talla

Kauyen na Karma dai na kusa ne da iyakar Burkina Faso da Mali, inda daruruwan mutane ke zuwa domin hakar Zinare ba bisa ka’ida ba.

Wasu mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewar sun ga tashin hankalin ne tun a ranar Alhamis da ta gabata, to amma labarin bai samu fita ba sai a jiya Lahadi.

Wadanda suka tsira daga farmakin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, ‘yan ta’addan fiye da 100 ne haye kan Babura da motoci suka kai hari kauyen nasu, kuma adadin wadanda suka kashe zai kai kimanin mutane 80 sabanin 60 da aka bayyana.

A ‘yan watannin baya bayan nan dai, hare-haren ‘yan ta’adda na karuwa a Burkina Faso, wadda tun shekarar 2015 take fafutukar murkushe su, tun bayan da mayakan masu ikirarin jihadi suka tsallaka cikin kasar daga makwafciyar ta Mali.

Ko a makon jiya gungun ‘yan ta’addan sun kashe jami’an tsaron sa-kai 34 da sojoji shida a wani hari da suka kai a kusa da kauyen Aorema a lardin na Yetanga.

Bayan harin ne, gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta ayyana dokar daukar sabbin sojoji, wadda ta shafi duk wani matashi da ya haura shekaru 18 a kasar

Gabanin waccan sanarwar ce kuma gwamnatin Burkina Faso ta sanar da shirin daukar karin sojoji 5,000 domin yakar ta'addancin da ya addabi kasar tun shekara ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.