Isa ga babban shafi

An yi jana'izar dakarun Burkina Faso 27 da 'yan ta'adda su ka kashe

Dubban mutane ne suka taru a Ouagadougou babban birnin Burkina Faso a ranar Asabar, domin jana'izar sojoji 27 da ‘yan ta’adda suka kashe, a wani harin kwanton bauna da suka kai musu a cikin watan da ya gabata.

Sojojin Burkina Faso tsaye a kusa da akwatunan gawarwakin 'yan uwansu 27 da 'yan ta'adda suka kashe, yayin kwanton Baunar da suka yi musu a ranar 26 ga watan Satumba.
Sojojin Burkina Faso tsaye a kusa da akwatunan gawarwakin 'yan uwansu 27 da 'yan ta'adda suka kashe, yayin kwanton Baunar da suka yi musu a ranar 26 ga watan Satumba. © REUTERS/Vincent Bado
Talla

An dai yi amfani da tutar kasar wajen nade akwatunan gawarwakin sojojin da suka rasa rayukan na su a ranar 26 ga watan Satumba, yayin da suke rakiyar ayarin motocin da ke jigilar kayayyaki zuwa garin Djibo da ke arewacin kasar, wanda mayaka masu ikirarin jihadi suka yi wa kawanya.

A ranar 30 ga watan Satumba, kwanaki hudu bayan harin, sojoji karkashin jagorancin Kaftin Ibrahim Traore suka hambarar da shugaba Paul-Henri Damiba, wanda suka ce ya gaza wajen dakile matsalar ta’addanci da ta sanya ya yi nasa juyin mulkin a watan Janairun da ya gabata.

A halin da ake ciki, batun girmama sojojin da suka mutu ya zama jiki a Burkina Faso, sakamakon yadda kasar ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyoyin IS da al Qaeda.

Tun bayan fara kaddamar da hare-hare a shekarar 2015, mayakan sun kashe dubban mutane tare da tilastawa wasu fiye da miliyan biyu tserewa daga gidajensu.

A watannin baya-bayan nan dai, masu tada kayar baya sun killace wasu sassan arewacin kasar ta Burkina Faso, lamarin da ya janyo karancin abinci ga dubban mutane, musamman a garin Djibo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.