Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kaddamar da shirin yaki da ta'addancci

Burkina Faso ta sanar da kaddamar da yaki da ta’addanci da kakkabe ‘yan ta’adda gadan-gadan a kasar. Wanda zai tilaswa duk dan kasar da ya kai shekaru 18 shiga aikin soja don yakin kare kasar. 

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traoré kenan.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traoré kenan. © AFP/Olympia de Maismont
Talla

Gwamnatin sojin kasar ta ce karkashin wannan sabuwar kadddamarwa zata yi duk mai yiwuwa wajen kakkabe ‘yan ta’adda daga kasar ta kowanne irin hali. 

Ko da yake jawabi, shugaban gwamnatin sojin kasar Ibrahim Traore ya ce sojoji zasu yi amfani da karfin da suke da shi wajen kwato kaso 40 na fadin kasar da ke hannun ‘yan ta’adda na kungiyoyin Al-Qaeeda da kuma IS. 

Har yanzu dai gwamnatin kasar bata fitar da cikakken rahoto game da tsare-tsaren da zata bi wajen wannan aikin ba, kawai dai ta gargadi ‘yan ta’addar su kuka da kansu. 

Karkashin wannan aiki, Burkina Fason zata dauki Karin sojoji dubu 5 nan take, kafin kuma shigar matasa na tilas, duk a kokarin da take yi na raba kasar da ayyukan ta’addanci. 

Wannan sabon shiri dai watakila baya rasa nasaba da kisan da ‘yan ta’adda ke yi a baya-bayan nan, don kuwa ko a makon da ya gabata sai da suka hallaka mutane 44 nan take a harin da suka kai kan wani kauye da ke arewacin kasar, hari mafi muni da aka gani cikin ‘yan makonnin nan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.