An tsawaita dokar ta baci da aka sanya a yankunan Burkina-Faso
Burkina Faso, kasar da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ta sanar da tsawaita dokar-ta-baci da da ta kakaba a kan yankuna 13 na kasar da karin watanni 6 tun a daga karshen watan Maris.
Wallafawa ranar:
Minstar shari’ar kasar, Bibata Nebie Ouedraogo ta ce gwamnati ta dau wannan mataki ne don jaddada nasararta a yakin da take da ta’addanci.
Gwamnatin kasar ta sanya dokar ta baci a yankunan da da rikicin ta’addanci ya fi shafa ne tun a watan Maris na shekarar da ta gabata.
Burina Faso, wadda sojoji suka kwace ragamar mulkinta a shekarar 2022 tana fama da matsalar ‘yan ta’addda masu ikirarin jihadi da ke shiga kasar daga Mali tun daga shekarar 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu