Isa ga babban shafi

Mnangagwa ya yi godiya ga al'ummar Zimbabwe kan zaben shi a wa'adi na 2

Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe ya sake lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye kodayake bangaren adawar kasar ya yi zargin tafka magudi gabanin fitar da sakamakon zaben.

Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe.
Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe. AFP - JEKESAI NJIKIZANA
Talla

Sakamakon da hukumar zaben ta Zimbabwe ta fitar a daren Asabar din da ta gabata ya nuna cewa Mnangagwa ya lashe kashi 52 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada yayin da abokin adawarsa Nelson Chamisa ya lashe kashi 44 wanda ke nuna cewa bai samu karin magoya baya daga yawan wadanda suka zabe shi shekaru 5 da suka gabata ba.

Sakamakon hukumar zaben ya nuna cewa jumullar kashi 69 na yawan masu katin zabe a Zimbabwe ne suka kada kuri’a a zaben wanda shugaba Mnangagwa ya bayyana a matsayin manuniya ga yadda kasar ke ci gaba da rungumar tsarin demokradiyya.   

Ko a shekaru 5 da suka gabata ma yayin zaben Zimbabwe na shekarar 2018 Mnangagwa ya lashe kashi 50.8 na yawan kuri’un da aka kada ne yayinda Chamisa ya lashe kashi 44.3.

A jawabin godiya da ya gabatar jiya Lahadi bayan sanar da sakamakon zaben, shugaba Emmerson Mnangagwa ya sha alwashin ci gaba da aiki tukuru don fitar da kasar daga tarin matsalolin da suka dabaibayeta.

Kazalika ya yi godiya da jajircewarsu wajen tabbatar da dorewar demokradiyyar a kasar da kuma ci gaba da jagorancin jam’iyyar ZANU-PF.

Wannan nasara ta Mnangagwa na nuna cewa har zuwa yanzu jam’iyya guda ke ci gaba da mulkar Zimbabwe tun bayan samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.