Isa ga babban shafi

Birnin Timbuktun kasar Mali ya koma karkashin ikon 'yan ta'adda

Masu tayar da kayar bayan, sun kwace ikon tsohon birnin Timbuktu na kasar Mali na tsawon kwanaki.

Dakarun Minusma a sansanin de Gani-Do, da ke yankin Dogon a tsakiyar kasar Mali kenan, yayin da suke binciken abubuwan fashewar da aka dasa. An dauki hoton ne ranar 4 ga watan Yuli, 2019.
Dakarun Minusma a sansanin de Gani-Do, da ke yankin Dogon a tsakiyar kasar Mali kenan, yayin da suke binciken abubuwan fashewar da aka dasa. An dauki hoton ne ranar 4 ga watan Yuli, 2019. © AFP / MARCO LONGARI
Talla

Mayakan sun toshe dukkanin hanyoyin shiga da wajen arewacin birnin da ke gefen hamadar sahara, kamar yadda wani dan majalisar dokokin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Wani mai gidan mai ya ce karin farashin yana yin tasiri sosai, domin kuwa litar mai ta tashi daga 845 na CFA zuwa 1,250 na CFA a cikin mako guda.

A farkon wannan watan, sakonnin kafofin sada zumunta da aka danganta ga wani kwamandan kungiyar da ke da alaka da Al Qaeda ya ayyana yaki a yankin Timbuktu.

Sakonnnin sun gargadi manyan motocin da suka fito daga kasashen Aljeriya, Mauritania da sauran wurare a yankin da kada su shiga cikin birnin.

Barazanar ta zo ne a cikin watan da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ta gabatar da janyewarta daga wani sansani da ke arewacin kasar, bisa la'akari da yanayin tsaro.

Kasar da ta fuskanci juyin mulki sau uku a cikin shekaru goma, tana karkashin mulkin soja ne da ke matsa lamba ga tawagar MINUSMA ta Majalisar Dinkin Duniya ta fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.